Syria

Mayakan IS sun kashe fararen hula 116 a Syria

Dakarun gwamnatin Syria a wani wurin bincike da ke Aleppo, watan yulin 2017.
Dakarun gwamnatin Syria a wani wurin bincike da ke Aleppo, watan yulin 2017. Reuters/路透社

Mayakan IS sun kashe fararen hula 116 a garin al-Qaryatayne da ke tsakiyar Syria, lokacin da mayakan ke kokarin tserewa daga farmakin dakarun gwamnati.

Talla

Shugaban kungiyar da ke sa-ido daga London kan abubuwan da ke farwa a Syria Rami Abdel Rahman, ya ce kisan ya faru ne a cikin kwanaki 10 da aka kwashe ana kokarin fatattakar mayakan daga wannan gari.

Mafi yawa daga cikin wadanda aka kashen, ‘yan bindigar na zargin su ne da hada baki da dakarun gwamnati domin tsegunta ma su sirrin mayakan kamar dai yadda shaidu suka tabbatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.