Saudi-Qatar

Sarkin Qatar ya ce mahukuntan Saudiyya na neman bayansa

Sarkin Qatar Sheikh Tamin bin Hamad Al-Thani
Sarkin Qatar Sheikh Tamin bin Hamad Al-Thani REUTERS/Hamad I Mohammed

Sarkin Qatar Sheikh Tamim bin Hamad Al-Thani ya zargi Saudiyya da kawayenta da yunkurin kifar da gwamnatinsa domin kawo sauyi a kasar.

Talla

A wata hirar da ya yi da tashar talabijin ta CBS da ke Amurka, Sarkin ya ce ba yau mahukuntan Saudiyya suka fara wannan ba, domin ko a shekarar 1996 lokacin da mahaifinsa ya karbi ragamar tafiyar da kasar sun bukaci yin haka.

Rikici tsakanin Qatar da Saudiyya ya barke ne a ranar 5 ga watan Yuni, kuma har yanzu bangarorin biyu sun kasa zaunawa kan teburi guda domin tattauna matsalar domin shawo kanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.