Iraqi-Kurdistan

Shugaban Kurdawan Iraki Barzani zai sauka daga mukaminsa

Shugaban yankin Kurdistan na Iraki, Massoud Barzani.
Shugaban yankin Kurdistan na Iraki, Massoud Barzani. REUTERS/Azad Lashkari

Shugaban yankin Kurdawan Iraki Massaoud Barzani ya ce zai sauka daga mukaminsa, sakamakon abubuwan da suka biyo bayan zaben raba-gardamar neman ‘yancin kan yankin da aka yi cikin watan jiya.

Talla

Barzani ya bayyana wannan mataki ne a gaban ‘yan majalisar dokokin yankin a jiya lahadi.

Yanzu haka dai gwamnatin Iraki na ci gaba da amfani da karfin soji, domin kwace wasu muhimman yankunan da ke da arzikin man fetur a kusa da iyakar yankin na Kurdistan da Iraki, yayin da Barzani ke shan suka dangane da gazawarsa wajen kare makomar kuri’ar raba gardamar da al’ummar yankin suka yi a cikin watan na jiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.