Falasdinu

Hamas ta mikawa Falasdinu ragamar tafiyar da iyakoki

Shugaban yankin Falasdinu Mahmoud Abbas
Shugaban yankin Falasdinu Mahmoud Abbas REUTERS/Carlo Allegri

Kungiyar Hamas ta mika wa gwamnatin Falasdinu ragamar tafiyar da hanyoyin da ke sada yankin da kasashen Masar da kuma Isra’ila, kamar dai yadda yarjejeniyar sulhun da aka kulla tsakanin Fatah da kungiyar ta Hamas a cikin watan jiya ta shata.

Talla

Mika sha’anin kula da wadannan wurare a hannun gwmanatin Mahmoud Abbas na nufin cewa Hamas ta dau hanyar cika alkawarin da ke kunshe a wannan yarjejeniyar wadda ta kawo karshen sabanin shekaru 10 da ke tsakanin bangarorin biyu.

Har ila yau wannan mataki na nufin cewa gwamnatin Mahmoud Abbas da yanzu ke zaune a birnin Ramallah, sannu a hankali za ta karbe iko da sauran lamurran da suka shafi yankin na Gaza wanda ke da mutane sama da milyan daya da rabi, amma kuma ke karkashin kawanyar Isra’ila.

A wannan laraba an gudanar da wani kwarya-kwaryan biki a mashigin Rafah wanda ita ce hanya daya tilo da ke hada Masar da yankin na Gaza, inda Mufeed Al-husayna, daya daga cikin ministocin Falasdinu da ya halarci bikin ke cewa wannan wata alama ce da ke nuni da hadin-kai tsakanin al’ummar Falasdinu baki daya.

A lokacin wannan biki, an sauke tutar Hamas tare da dora ta Falasdinu da Masar da kuma wani katon hoton shugaba Mahmoud Abbas da aka rataye a kofar mashigin na Rafah.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.