Rasha-Syria

Rasha ta yi watsi da rahoton amfani da makami mai guba a Syria

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin Reuters

Rasha ta yi watsi da rahotan Majalisar Dinkin Duniya da ya zargi gwamnatin Syria da amfani da makamai mai guba kan fararen hula a harin da dakarun ta suka kai Khan Sheikun.

Talla

Shugaban sashen tsaro da kwance makamai na ma’aikatar harkokin wajen Rasha, Mikhail Ulyanov ya ce sun gano cewar rahotan labarin kanzon kurege ne da wasu wadanda basu kware ba suka rubuta shi ba tare da zuwa inda aka samu matsalar ba.

Wani kwamiti da ya kunshi jami’an diflomasiya da jami’an tsaro ya gabatar da rahoton binciken da Rasha ta gudanar tare da hotuna wanda ke nuna cewar ba gwamnatin Rasha ce ta kai harin da ya hallaka mutane sama da 80 ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.