Syria-Iraqi

Dakarun Iraqi sun kori IS daga yankin Deir Ezzor

Mayakan Syria yan lokuta da kama wasu yankunan dake hannun yan tawayen Is .
Mayakan Syria yan lokuta da kama wasu yankunan dake hannun yan tawayen Is . 路透社。

Dakarun Syria da Iraqi sun yi nasarar kwace birnin Deir Ezzor, gari mafi girma da ya rage a hannun mayakan IS sakamakon wasu jerin hare hare da suka kaddamar akan su.

Talla

Gwamnatin Syria ta sanar da samun nasara da taimakon Rasha wadda jiragen yakin ta ke marawa sojojin kasar baya, yayin da sojin Iraqi suka kwace garin Husaybah dake kan iyaka.

Kakakin sojin Iraqi ya tabbatar da cewar yanzu haka a mayar da doka da oda a Yankin.

A lokacin da Gwamnatin Syria ta sanar da samun nasara,‘yan gudun hijirar Syria da yanzu haka ke zaune a kasar Girka da dama ne suka shiga yajin cin abinci a birnin Athens, domin nuna rashin amincewarsu dangane da yadda mahukuntan kasar suka haramta wa sauran ‘yan uwansu sama da dubu biyu damar ganawa da ‘yan uwansu da ke zaune a wani bangare na kasar ta Girka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.