Syria

Mayakan IS sun hallaka 'yan gudun hijira 75

Wasu 'yan gudun hijirar kasar Syria da suka tserewa rikicin Dier Ezzor.
Wasu 'yan gudun hijirar kasar Syria da suka tserewa rikicin Dier Ezzor. Yahoo

Wani harin bam da aka dana a mota ya hallaka yann gudun hijira 75, ciki harda kananan yara a gabashin kasar Syria.

Talla

Rami Adel Rahman, shugaban kungiyar sa ‘ido kan yakin Syria, ya bada tabbacin cewa mayakan IS ne suka kai harin wanda ya jikkata wasu ‘yan gudun hijirar 140.

‘yan gudun hijirar sun tserewa fadan da ake gwabzawa ne tsakanin sojin Syria da ‘yan tawaye a lardin dier Ezzor.

Kungiyar bada agaji da Save the Children ta ce akalla mutane dubu 350,000 ne suka tserewa fadan da ake a lardin na Dier Ezzor, kuma rabinsu kananan yara ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.