Lebanon

Shugaban Lebanon ya gana da manyan jami'an tsaro

A karshen mako ne Saad Hariri ya yi murabus
A karshen mako ne Saad Hariri ya yi murabus REUTERS/Mohamed Azakir

Bayan murabus din firaminista Saad Hariri, shugaban kasar Lebanon, Michel Aoun ya gana da manyan shugabanin tsaron kasar domin tabbatar da zaman lafiya.

Talla

Shugaban ya shaida wa jami’an muhimmancin tabbatar da zaman lafiya da kuma kauce wa daukar duk wani mataki da zai jefa kasar cikin rikici.

A karshen mako, Saad Hariri ya sanar da saukar sa daga mukamin, a wani jawabi da ya yi daga Saudi Arabia ta kafar talabijin, inda ya zargi Iran da yin barazana ga rayuwarsa.

Tuni Iran ta nesanta kan ta daga zargin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.