Yemen

Saudiyya ta bude bakin iyakar Yemen domin shigar da abinci

Mutane sun taru a wani wurin da aka kai hari a Arhab arewacin Sanaa.
Mutane sun taru a wani wurin da aka kai hari a Arhab arewacin Sanaa. REUTERS/Khaled Abdullah

Hukumomi a kasar Yemen sun ce dakaru karkashin jagorancin Saudiyya, masu fada da ‘yantawayen Houthi sun sake bude bakin iyaka na al Wadea mai matukar muhimmanci.

Talla

Rufe wannan iyaka da aka yi a farkon makon nan, ya sanya majalisar dinkin duniya ta nuna damuwarta kan ukubar yunwa da ka iya afka wa kasar ta Yemen.

A ranar litinin din da ta gabata ne dai dakarun, wadanda ke karkashin jagoranci kasar Saudiyya suka kulle mashigar ta sama, da ruwa, da kuma ta kasa, bayan Saudiyya din ta kabo wani makami wanda ake tunanin cewa ‘yantawayen Houthi ne suka harba shi zuwa Riyadh.

Hukumomi da kuma wadanda suka shaida da idanunsu sun bayyana cewa mashigar ta al Wadea, wacce ta hada Saudiyya da gabacin kasar, an bude ta ne a ranar alhamis, ta yadda za a samu damar shigewa da kayan abinci da sauran kayan masarufi zuwa cikin kasar ta Yemen.

A baya dai majalisar dinkin duniya ta ce rufe iyakan zai iya haifar da yunwa wacce za ta kashe miliyoyin mutane a kasar ta Yemen. Wadda kuma majalisar ta dinkin duniya ta bayyana a matsayin yunwa wacce za ta fi kowace muni a doron kasa.

‘Yan tawayen na Houthi dai akasarinsu sun fito ne daga mabiya akidar shi’a ta Zaidi, marasa rinjaye, da kuma wasu magoya bayan tsohon shugaban kasar Ali Abdallah Saleh.

A halin yanzu dai 'yanadawan ne ke iko da mafi yawan yankunan kasar ta Yemen, wanda ya hada har da San’aa, babban birnin kasar.

Kasar Saudiyya da sauran kawayenta na yankin larabawa ne suka daura yaki da ‘yantwayen na Houthi saboda goyon bayan da suke yi wa gwamnatin shugaba Abd-Rabbu Mansour Hadi, wacce yanzu haka ke da mazauni a birnin Aden.

Gwamnatin Saudiyya dai na zargin cewa ‘yantawayen na Houthi na samun makamai ne daga hannun kasar Iran, zargin da Iran din ta musanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.