Iraqi

Sojin Iraqi sun kaddamar da sabon farmaki kan IS

Sojojin kasar Iraqi a kan tankokin yaki.
Sojojin kasar Iraqi a kan tankokin yaki. REUTERS/Stringer

Sojin Iraqi sun kaddamar da wani sabon farmaki domin kwato garin Rawa, da ke hannun mayakan IS, wanda shi ne karamin yanki na karshe da ke karkashin ikon kungiyar.

Talla

Idan har farmakin wanda aka kaddamar a wannan rana ta Asabar ya yi nasara, zai kara sanya mayakan kungiyar ta IS cikin munin yanayi na fuskantar murkushewa baki daya a fadin kasar Iraqi.

Rawa, daya ne daga cikin garuruwan da suke kan iyakar kasar Iraqi da Syria, wadanda kungiyar IS ta tsara, ko ta yi ikirarin zasu kasance a karkashin katafaren lardin da zata kafa na “Euphrates”, wanda ke da muhimmanci a wajenta, kasancewar tana amfani da hanyoyin yankin, wajen safarar makamai, da abinci a tsakanin Syria da Iraqi.

A halin yanzu, sojin Iraqi, sun samu nasarar korar mayakan IS daga akalla kashi 95 na fadin lardin Euphrates, inda suke fafutukar kafa mulkinsu a baya, hakan ya bai wa ‘yan kasar ta Iraqi sama da miliyan 4 samun ‘yanci daga karkashin mulkin mayakan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.