Zanga-zanga ta balle a kasashen Larabawa kan birnin Qudus
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar:
Falasdinawa da kuma al’umma a kasashen larabawa, a ranar Juma’a sun yi zanga-zangar nuna adawa da matakin shugaban Amurka Donald Trump na ayyanan birnin Qudus a matsayin babban birnin Isra’ila.
Bayan gabatar da sallar Juma’a an samu tashe-tashen hankula a tsohon birnin Qudus da sauran garuruwa irin su Bethlehem, da Hebron da kuma Nablus.
A wasu yankunan, Falasdinawa sun rinka jefa duwatsu a kan jami'an tsaro, su kuma jami’an tsaro sun mayar da martani da harba harsasan roba da barkono mai sa hawaye.
Sauran kasashen da aka yi zanga-zangar sun hada da Malaysia, inda mutane suka taru a gaban ofishin jakadanci Amurka da ke birnin Kuala Lumpur domin nuna adawarsu da matakin.
Haka nan ma a kasashen Masar, da Afghanistan, da Tunisia da kuma Turkiyya, masu zanga-zanga sun rinka yin kalaman nuna kiyayya ga matakin na Amurka.
Ma'aikatar lafiya ta Falasdinu ta ce sojojin Isra'ila sun harbe bafalasdine daya har lahira, sannan sun raunata mutane da dama a sanadiyyar amfani da harsasan roba da barkono mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zanga.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu