Gabas ta tsakiya

Larabawa sun buƙaci Trump ya janye matsayarsa kan Qudus

Matakin Amurka kan Qudus ya haifar da jerin zanga-zanga a kasashen Larabawa.
Matakin Amurka kan Qudus ya haifar da jerin zanga-zanga a kasashen Larabawa. Probst/ullstein bild via Getty Images

Ministocin harkokin waje na ƙasashen Larabawa sun bukaci Donald Trump na Amurka da ya janye matakin da ya ɗauka na ayyana Qudus a matsayin babban birnin Irsa’ila.

Talla

Sannan sun buƙaci ƙasashen duniya da su amince da wanzuwar ƙasar Falasɗinu tare da amincewa da gabashin birnin Qudus a matsayin fadar ƙasar.

A matsayar da suka cimma, bayan kammala wani taron gaggawa da ministocin suka yi ranar Asabar a Alƙahira, babban birnin Masar, ministocin sun ce yanzu haka Amurka ta nuna wa duniya cewa ba ta cancanci zama mai shiga tsakani ba a rikicin na Falasɗinawa da Yahudawa.

Ministocin sun yi fatali, tare da Allah-wadai da matakin na Amurka.

Matakin na Amuraka na cigaba da haifar da bore a ƙasashen na Larabawa, inda masu zanga-zanga ke nuna goyon bayan su ga yankin Falasɗinu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.