Isra'ila

Netanyahu ya soki kasashen Turai

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu. REUTERS/Gali Tibbon/Pool

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce ba zai amince da abinda ya kira munafinci na ƙasashen Turai ba, dangane da matakin Amurka na ayyana Qudus a matsayin fadar gwamnatin ƙasarsa.

Talla

Netanyahu ya yi wannan furuci ne a ranar Asabar, gab da baluguron da yanzu haka yake yi zuwa Faransa domin ganawa da shugaba Emmanuel Macron da kuma taron da zai yi da ministocin harkokin waje na ƙasashen Turai a birnin Brussels.

Ya ce a sa’ilin da yake jin ƙasashen na kushe matakin Amurka kan amincewa da Qudus a matsayin babban birnin Isra’ila, bai ji wani ya fito ya yi tir da hare-haren roka da aka kai wa Isra’la ba.

Ya ce duk da ya na martaba ƙasashen na Turai, to amma ba zai lamunci fuska-biyu da suke nunawa game da rikicin na yankin gabas ta tsakiya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI