Isa ga babban shafi
Syria

‘Yan gudun hijirar Syria a Lebanon na cikin yunwa

'Yan gudun hijirar Syria a Lebanon na cikin talauci
'Yan gudun hijirar Syria a Lebanon na cikin talauci Reuters/Aziz Taher
Zubin rubutu: Umaymah Sani Abdulmumin
1 min

Majalisar Dinkin Duniya ta ce yanzu haka sama da rabin 'yan gudun hijirar Syria da suka samu mafaka a kasar Lebanon na fama da tsananin yunwa, yayin da akasarin su na rayuwa cikin tsananin talauci.

Talla

Alkaluman Majalisar Dinkin Duniya sun nuan cewar, mutane sama da miliyan guda ne suka samu mafaka daga kasar Syria a Lebanon tun bayan barkewar yakin kasar a watan Maris na shekarar 2011.

Mirelle Girard, jami’ar Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar a Lebanon ta ce akasarin 'yan gudun hijirar sun dogara ne da taimakon da suke samu daga kasashen duniya wanda tuni ya ragu.

Rikicin kasar Syria ya yi sanadiyar mutuwar mutane sama da 340,000, yayin da sama da miliyan 5 suka gudu suka bar kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.