Saudiya

'Mayakan Huthi sun harba roka Saudiya'

'Yan tawayen Huthi a Yemen
'Yan tawayen Huthi a Yemen AFP PHOTO / MOHAMMED HUWAIS

Kasar Saudi Arabia ta ce ta kakkabo wani makamin roka da ‘Yan Tawayen Huthi da ke Yemen suka harba zuwa Riyadh.

Talla

Kamfanin dillancin labaran Faransa ya ce an harba makamin ne da misalin karfe 10.50 a dai-dai lokacin da ake shirin gabatar da kasafin kasar a fadar Yamamah.

Saudi Arabia ta bayyana cewar makamin na Huthi kirar kasar Iran ne.

Wannan shine karo na 2 da ‘yan tawayen ke harba irin wannan makami a cikin watanni biyu. A shekara ta 2014 mayakan Huthi suka karbe ikon birnin Yemen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.