Isa ga babban shafi
Iran

Rouhani na ziyarar aiki a India

Shugaban kasar Iran Hassan Rohani tare da Firaministan India Narendra Modi.
Shugaban kasar Iran Hassan Rohani tare da Firaministan India Narendra Modi. REUTERS
Zubin rubutu: Azima Bashir Aminu
Minti 2

Shugaban Iran Hassan Rohani ya fara ziyarar aiki ta tsawon kwanaki uku a India domin habaka kasuwanci da kuma musayar fasaha a bangaren makamashi tsakanin kasashen biyu.

Talla

Ziyarar shugaban ta farko zuwa India tun bayan hawansa mulki za ta dauke shi tsawon kwanaki 3 ta yadda za su tattauna muhimman batutuwa da suka shafi huldar kasuwancin da ke tsakaninsu kafin komawarsa gida a ranar Alhamis din makon nan.

Akwai dai kyakkyawar alaka a tsakanin kasashen biyu, tun daga lokacin da Firaministan India Nerendra Modi ya ziyarci Iran a shekara ta 2016, inda shugabannin biyu suka kaddamar da gina wata tashar jiragen ruwa a Chabahar kudu maso gabashi Iran.

Haka zalika India na daga cikin jerin manyan kasashe uku da ke ci gaba da sayen man fetur din Iran ko a lokacin da takunkuman Amurka ke tsaka da aiki  akan Iran.

A lokuta da dama dai kasashen biyu kawayen juna kan tsoma baki kan al'amuran cikin gidan junansu kamar yadda ya faru a bara Inda jagoran addinin Iran Ayatollahi Khamene'i ya tsoma baki kan takaddamar yankin Kashmir da India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.