wasanni

An kama dan wasan Japan da shan kwayoyi a Olympics

Dan wasan tseren kankara na Japan ya yi amfani da kwayoyi masu kara kuzari a gudun mita dubu 1 da dari biyar.
Dan wasan tseren kankara na Japan ya yi amfani da kwayoyi masu kara kuzari a gudun mita dubu 1 da dari biyar. google.com

Hukumar kula da wasannin Olympics ta duniya ta dakatar da dan wasan tseren kankara na kasar Japan Kei Saito daga shiga wasannin Olympics da ke ci gaba da gudana a Korea ta kudu bayan gano shi da amfani da wasu kwayoyi masu kara kuzari.

Talla

Tuni dai Saito mai shekaru 21 ya tattara kayansa ya bar filin wasan, sai dai hukumar ta ce za ta kara gudanar da bincike da zai bata damar dakatar da shi daga shiga duk wani wasannin Olympics a duniya, matukar aka gano cewa ya dade yana amfani da kwayoyin.

Saito dai shi ne ya zo na uku a bangaren tsere kan dusar kankara a 2013 da kuma 2014, haka zalika yana cikin ‘yan wasan da Japan ke ji da su, don ko a ranar asabar ma ya lashe tseren kankarar mai nisan mita dubu 1 da dari biyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI