Amurka zata maida ofishin jakadancinta zuwa Kudus a watan Mayu
Wallafawa ranar:
Amurka ta ce cikin watan Mayu mai zuwa zata bude ofishin jakadancinta na Isra’ila a birnin Kudus, kamar yadda ta alkawarta dauke ofishin jakadancin daga birni Telaviv.
Shugaban Amurka Donal Trump ne ya sanar da matakin a birnin Washington yayin gabatar da jawabi ga wasu magoya bayansa.
A watan Disambar bara shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da goyon bayan mayar da birnin na Kudus zama babban birnin kasar Isra’ila, matakin da ya fusata, Falsadinawa, kasashen Musulmi, kungiyar tarayyar turai da sauran kasashen da ke ganin shawarar zata dagula yunkurin kawo karshen rikicin Isra’ila da Falasdinu.
Sanarwar ta Amurka ta zo a bazata, kasancewar a watan janairu da ya gabata, mataimakin shugaban Amurka Mike Pence, ya shaidawa majalisar Isra’ila cewa za’a bude sabon ofishin jakadancin ne a karshen shekarar 2019.
Tuni shugaban yankin Falasdinawa Mahmoud Abbas, ya bayyana matakin na Amurka a matsayin abin da zai dakile yunkurin samar da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu