Syria

Kwamitin Sulhu zai kada kuri'a kan tsagaita yakin Syria

Wasu mutane a garin Douma, dake gabashin yankin Ghouta, a Syria, yayin da suke kallon kwanson wani makami mai linzami da aka kai hari da shi a yankin. 23, Fabarairu, 2018.
Wasu mutane a garin Douma, dake gabashin yankin Ghouta, a Syria, yayin da suke kallon kwanson wani makami mai linzami da aka kai hari da shi a yankin. 23, Fabarairu, 2018. REUTERS/Bassam Khabieh.

Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya a jiya Juma’a, ya jinkirta kada kuri’a kan tsgaita wuta a Syria tsawon kwanaki 30 a ranar Juma'a da ta gabata, don dakatar da luguden wutar jiragen yakin gwamnati da na Rasha kan yankunan ‘yan tawaye, musamman a yankin gabashin Ghouta.

Talla

Jinkirin kada kuri’a kan kudurin da kasashen Sweden, da Kuwaiti suka gabatar, ya biyo bayan, kawo sauyi a kudirin tsarin shigar da kayayyakin agaji da kwashe fararen hula a yankin na Ghouta mai fama da hare-haren dakarun gwamnati da Rasha ta yi.

A halin yanzu wani lokaci a yau Asabar ake sa ran kwamitin sulhun ko na tsaron Majalisar Dinkin Duniyar mai manbobi 15, zai kada kuri’a kan tsagaita yakin na Syria.

Yankin gabashin Ghouta da ke hannun ‘yan tawaye, ya kasance cikin kawanyar sojin gwamnatin Syria, tun a shekarar 2013, lamarin da ya haifar da matsalolin karancin kayan abinci, ruwan sha da wutar lantarki, da suka kara tabarbarewa a shekarar da ta gabata ta 2017.

Hasarar rayukan fararen hula a yankin na Ghouta, shi ne mafi muni da aka taba gani a yakin Syria tun bayan kwace wasu yankunan birnin Aleppo daga ‘yan tawaye a 2016.

Zuwa yanzu sama da fararen hula 462 suka rasa rayukansu a yankin na gabashin Ghouta, ciki har da kananan yara 99, wasu daruruwa kuma suka jikkata, sakamakon farmakin da jiragen yakin Syria ke kai wa ‘yan tawaye.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.