Syria

EU ta bukaci cimma sahihiyar yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria

Wani sashi na garin Douma da jiragen yakin Syria suka yi wa barin wuta, a gabashin yankin Ghouta, a Syria. 23 ga Fabarairu, 2018.
Wani sashi na garin Douma da jiragen yakin Syria suka yi wa barin wuta, a gabashin yankin Ghouta, a Syria. 23 ga Fabarairu, 2018. REUTERS/Bassam Khabieh

Kungoyar Turai na cigaba da yi wa kasashen Rasha, Iran da kuma Turkiyya matsin lamba, domin ganin cewa dakarun gwamnatin Syria sun dakatar da hare-haren da suke kai wa garin Ghouta da ke gabashin birnin Damascus.

Talla

Shugabar ofishin kare manufofin ketare ta Kungiyar Turan Federica Moghereni, ta bukaci kasashen su yi amfani da matsayinsu domin cimma sahihiyar yarjejeniya ta tsagaita wuta a yankin na ‘yan tawaye.

Moghereni, ta ce fararen hula da ke rayuwa a yankin na Ghouta, suna cikin kunci, saboda haka ya kamata a gaggauta tsagaita farmakin da ake kai wa yankin domin samun damar isar ma su da kayyayakin jinkai.

Kungiyar ta Turai ta ce kasashen na Turkiya Iran da Rasha, na da alhakin dakatar da fadan, domin wannan na daga cikin muhimman kudurorin da aka cimma matsaya a kai a lokacin da aka gudanar a taro a birnin Astana.

A ranakun 24 da kuma 25 ga watan Afrilu mai zuwa, kungiyar ta Turai za ta karbi bakuncin taro don tattauna halin da ake ciki a Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.