China

Xi Jinpin na iya zama shugaban China na din-din-din

Shugaban kasar China Xi Jinping.
Shugaban kasar China Xi Jinping. REUTERS/Fred Dufour/Pool

Majalisar kasar China mai manbobi 2, 924, zata kada kuri’ar amincewa da soke tsarin wa’adi a shugabancin kasar, abinda zai bai wa Xi Jinping zama shugaban kasar ta China na din-din-din.

Talla

Daga shekarar 1990 China ta fara amfani da tsarin wa’adi biyu bisa shugabancin kasar.

Amma a karshen watan fabarairu da ya gabata, jam’iyyar kasar mai ra’ayin gurguzu da ke muki ta gabatar da bukatar soke bin tsarin wa’adin, abinda zai baiwa Xi Jin Ping damar cigaba da shugabanci bayan karewar wa’adinsa a 2023.

Duk dacewa ana kyautata zaton majalisar mai manbobi dubu 2, 924 zata amince da bukatar cikin sauki, akwai yiwuwar wasu da dama su kauracewa jefawa bukatar kuri’a.

Shugaban Amurka Donald Trump ya fara fuskantar suka bisa kalaman da ya yin a baya bayan nan, na goyon bayan yunkurin na bai wa Xi Jinpin damar zama shugaban China na din-din-din, inda ya ce babu mamaki suma Amurkawa su gwada yunkurin a nan gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI