China

China zata kare martabar ta a Duniya

XI Jinping Shugaban kasar China
XI Jinping Shugaban kasar China REUTERS/Etienne Oliveau/Pool/

Shugaban Kasar China Xi Jinping yayi gargadi dangane da duk wani yunkurin raba kasar, inda ya bayyana shirin kasar na shiga yaki domin kare martabar ta a duniya.

Talla

Yayin jawabi ga taron Majalisar kasar wadda ta bude masa kofar ci gaba da zama a karagar mulki har iya ran sa, shugaba Xi ya ce duk wani kokarin raba kasar ba zai yi tasiri ba, kuma yan kasar China za suyi Allah wadai da shi.

Shugaban yayi watsi da masu sukar yadda China ke fadada ayyukan cigaban ta a kasahsen duniya, inda yake cewa wadanda suka saba razana wasu kasashe ne kawai ke fargabar cigaban kasar kuma suke kallon matakin a matsayin barazana a gare su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.