China

China ta musanta rage kudin fito don magance yakin kasuwanci

Shugaban kasar China Xi Jinping.
Shugaban kasar China Xi Jinping. © Reuters

Kasar China ta musanta rahotan cewar shugaba Xi Jinping ya bayyana aniyar rage kudin fito domin rage tankiyar da ake samu tsakanin China da Amurka ta fannin kasuwanci.

Talla

Mai magana da yawun ma’aikatar kasuwancin China, Gao Feng ya ce har yanzu kasar a shirye ta ke ta ce cas, aduk lokacin da Amurka ta ce mata kule dangane da rikicin kasuwancin da ake samu.

Gao ya ce babu yadda China za ta zauna ta na zuba ido kan Amurka na gaban kanta wajen daukar matakan da suka sabawa dokokin duniya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya daura damarar kakaba wasu tarin haraji kan kayakin da Chinar ke shigarwa kasarsa a wani mataki da ake kallo da yakin kasuwanci.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.