Myanmar

Myanmar ta yafe wa hursunoni dubu 8 da 500

'Yan gudun hijirar Rohingya a Bangladesh
'Yan gudun hijirar Rohingya a Bangladesh 路透社。

Shugaban Kasar Myanmar Win Myint ya sanar da yin afuwa ga fursunoni 8,500 da suka hada da mutane kusan 40 da ake tsare da su saboda siyasa, albarkacin bukin al’adun gargajiyar na shekara-shekara da ake a kasar.

Talla

Shugaba Win Myint wanda ya fara aiki a watan jiya bayan ajiye aikin da ya gada, ya fadi cewa an yi wa mutanen afuwa ne saboda dalilan jinkai, a lokacin bukukuwan sabuwar shekara na mabiya Budda da aka fi sani da Thingyan.

An fi bada afuwan ne ga masu laifuka da suka shafi mu’amalla da miyagun kwayoyi, sannan kuma akwai wasu ‘yan kasashen waje 50 da wasu ‘yan siyasa 36.

Aung Myo Kyaw mai Magana da yawun kungiyoyin da ba na Gwamnati ba da ke taimakawa fursunoni, ya yaba da afuwar, amma ya nemi a sako wasu fursunoni 8 da ya dace a sake su amma kuma aka ki sakin su.

Ya bayyana cewa akwai mutane akalla 200 da ake tuhuma yanzu haka, saboda haka ya dace idan Gwamnatin da gaske take yi ta kori kararrakin da ke gaban kotu saboda zargin da ake yi masu.

Gwamnatin Myanmar dai ta salami dubban fursunoni da take tsare dasu, tun lokacinda ta mika mulki daga soja zuwa ga fararren hula.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI