India

An yi dokar hukuncin kisa ga masu yi wa mata fyade a India

Women protesting rape culture in India where victim shaming is rife
Women protesting rape culture in India where victim shaming is rife Reuters/Anindito Mukherjee

Gwamnatin kasar India ta amince da hukuncin kisa ga duk wanda aka sama da laifin yi wa kananan yara fyade, amincewa da wannan hukuncin kuwa ya zo ne bayan wani hadin guiwa da wasu samari suka yi suka yi wa wata yarinya yar shekaru 8 fyade baya ga wasu jerin laifukan da aka yi ta samu a baya.

Talla

Firaministan kasar Narendra Modi ne ya kira taron majalisar zartaswar kasar domin tattaunawa da kuma duba yiyuwar daukar matakin magance matsalar yawan fyade da ake samu a cikin kasar.

A baya dai an sha samun barkewar zanga-zanga a duk fadin kasar akan yadda ‘yan Addinin Hindu ke yi wa yara mata musulmi fyade a jihohin Jammu da Kashmir wani mataki na nuna cin zarafi ga al’ummar musulmin kasar, abinda ya kara kaimin matsin lamba da ake yi wa gwamnatin kasar akan bukatar a dakatar da matsalar tun btayi kamari ba.

A yau dai ne Majalisar kasar ta Indiya ta amince da gagarumin rinjaye kan batun yin gyara ga Dokar hana cin zarafi ta hanyar fasikanci, tare da kafa dokar hukunta duk wanda aka sama da cin zarafin ‘ya’ya mata daga shekaru 12 zuwa kasa.

A shekarar 2015 kadai an samu korafe-korafe na yi wa yara mata dubu 11 fyade a kasar ta India.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.