China

Hari da wuka ya hallaka kananan yara 7 a China

Wani mutum dauke da wuka a kasar China ya kai farmaki kan tarin daliban wata makaranta a lokacin da su ke shirin tafiya gida tare da kashe dalibai yara 7, baya ga raunata wasu.

Tarin jami'an tsaro kenan da aka girke a harabar makarantar bayan harin da ya hallaka dalibai.
Tarin jami'an tsaro kenan da aka girke a harabar makarantar bayan harin da ya hallaka dalibai. Reuters/路透社
Talla

Maharin wanda matashi ne da shekarunsa ba su wuce 28 ba, wanda aka yi ittifakin ya fito ne daga kauyen Mizhi na kasar tuni jami'an tsaro suka damke don amsa laifin da ya aikata.

Sai dai da ya ke bayyana dalilinsa na kai harin, matashin wanda aka bayyana sunanshi da Zhao ya ce ya kai farmakin ne don huce takaici tare da daukar fansa kan irin cin zarafin da aka yi masa lokacin da ya ke makaranta.

Kusan za a iya cewa harin wuka ba sabon abu bane a China, inda ko a watan Fabarairun da ya gabata ma sai da wani mutum ya hallaka wata mace ta hanyar daba mata wuka tare da jikkata wasu karin mutum 12 a wani shagon sayayya da ke Beijing.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI