Saudiyya na daukar matasa a matsayin sojin haya don ayyukan tsaro

Sauti 04:03
Wasu daga cikin jiragen yakin Saudiya da ke kai farmaki a Yemen.
Wasu daga cikin jiragen yakin Saudiya da ke kai farmaki a Yemen. FAYEZ NURELDINE/AFP

Daruruwan matasa ne daga kabilar Larabawa ko wasu kabilun dake jin Larabci a yankin kan iyakar da ta hada kasashen Tchadi Jamhuriyar Nijar da Libiya ne, wani kamfanin tsaro na kasar Daular Larabawa ke dauka sojojin haya da sunan tsaron wasu muhimman wurare a kasar Saudiya, musamman dakin Ka’aba mai tsarki, amma kuma a zahiri ake karkatar da su zuwa fagen yaki a kasar Yemen ba tare da saninsu ba.Matasan na karbar albashin da yawansa ya kama daga dalar Amruka 900 zuwa dubu 3000 a wata, alámarin da ya taimaka wajen saka daruruwan matasa amincewa kwangilar mai hadarin gaske.To ko ya ya masana tsaro ke kallon wannan alámari. Mahaman Salisu Hamisu ya tattauna da Maman Dan Buzuwa mai sharhi kan lamuran tsaro a jamhuriyar Nijer ga dai yadda firarsu ta kasance.