China

China na cigaba da tsare matar Liu Xiaoboo

Marigayi Liu Xiaobo na kasar China
Marigayi Liu Xiaobo na kasar China HRW

A kasar China, yan Sanda sun hana jakadun kasashen Faransa, Jamus , kungiyar tarrayar Turai da wasu kasashe biyu kaiwa matar marigayi Liu Xiaoboo mutumen nan da ya lashe kyautar Nobel na shekara ta 2010 ziyara a gidan ta.

Talla

Liu Xiaoboo marubuci wanda kotu a China ta yankewa hukuncin daurin shekaru 11 bisa laifin sake rubuta wani kundi da ya sabawa manufofin hukuma, ya rasu ya na mai shekaru 57 a Duniya bayan da yayi fama da Cancer a lokacin da yake tsare.

Jakadun wadanan kasashe sun sake jaddada fatar su na ganin hukumomin China sun janye matakin hana matar mamacin yawo ko balaguro, haka zalika kasar Jamus ta bakin jakadiyar kasar a China ta bayyana cewa Jamus na fatan baiwa matar Liu Xiaobo mafaka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.