Isa ga babban shafi

Faransa ta kwace kadarar wasu kamfanoni bisa alaka da makami mai guba

Wasu kananan yara yayin karbar magani a garin Douma na yankin gabashin Ghouta, bayan da harin makami mai guba ya rutsa da ita a watan Afrilu, 2018.
Wasu kananan yara yayin karbar magani a garin Douma na yankin gabashin Ghouta, bayan da harin makami mai guba ya rutsa da ita a watan Afrilu, 2018. White Helmets/REUTERS
Zubin rubutu: Nura Ado Suleiman
Minti 2

Ministan kudi na Faransa Bruno Le Maire, ya sa hannu kan takardar umarnin gwamnati na kwace ilahirin kadarorin wasu kamfanoni da ke kasar, tsawon watanni 6.

Talla

Faransa ta dauki matakin akan kamfanonin da hedikwatocinsu ke kasashen Syria, Lebanon da China, bayan bankado cewa suna da hannu wajen safara da kera makamai masu guba a Syria, da aka yi amfani da su wajen hallaka fararen hula a kasar.

A watan Janairu da ya gabata, Faransa ta hukunta wasu mutane 25 da kamfanoni da ke da hedikwata a Syria ta hanyar kwace musu kadarori da kakaba musu takunkumi, bisa zarginsu da taimakawa samar da makamai masu guba a kasar ta Syria.

A ranar Juma’ar da ta gabata wasu kasashe 30 suka gudanar da taro a Faransa, domin cimma matsaya akan bai hukumar sa ido kan makamai masu guba ikon bayyana bangarorin da ake zargi da amfani da makaman masu guba a dik lokacin da akai zargin amfani da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.