Syria-Amurka

Assad ya yi barazanar amfani da karfin soja akan Kurdawa

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad.
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad. Reuters

Shugaban Syria Bashar al-Assad yayi barazanar amfani da karfin soja akan Kurdawan dake samun goyan bayan Amurka, wadanda yanzu haka suke rike da kashi daya bisa uku na kasar.

Talla

Assad ya shaidawa wata kafar talabijin ta Rasha cewa yana fatan ganin an tattauna tsakanin gwamnati da Kurdawan, domin warware matsalar da ake samu, amma idan hakan ya faskara to fa zai yi amfani da karfi.

Shugaban ya kuma ce an kusa fuskantar yaki gaba da gaba tsakanin dakarun Amurka da Rasha lokacin da jiragen Amurka suka kai hari kusa da inda dakarun Rasha suke.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.