Diflomasiya

Babu abinda zai hana mu saida wa Qatar makamai - Rasha

Rasha ta yi watsi da adawar Saudiya kan saida wa Qatar makamin zamani na harbo jiragen yaki da makamai masu linzami kirar S-400.
Rasha ta yi watsi da adawar Saudiya kan saida wa Qatar makamin zamani na harbo jiragen yaki da makamai masu linzami kirar S-400. AFP Photo/Alexander Nemenov

Gwamnatin Rasha ta ce ba zata fasa saidawa Qatar makamin kakkabo jiragen yaki da makamai masu linzami ba kirar S-400 duk da zazzafar adawar da Saudiya ke yi da gudanar cinikin.

Talla

Shugaban kwamitin tsaro na majalisar kasar Aleksei Kondratyev, Saudiya ba ta da ikon kawo cikas ga sayar da Qatar makamin ballantana ta haramta shi.

A jiya Asabar ne dai, Sarkin Saudiya Salman ya yi barazanar daukar matakin soja akan Qatar muddin ta kuskura ta sayi makamin zamanin na harbor jiragen yaki da makamai masu linzami.

Cikin wasikar da ya aikewa shugaban Faransa Emmanuel Macron Sarki Salman ya ce mallakar makamin ga Qatar, barazana ce ga tsaron kasar ta Saudiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.