Iraqi ta kaddamar da sabon farmaki kan mayakan IS a Syria

Wani jirgin yakin Iraqi, yayin luguden bama-bamai akan mayakan kungiyar ISIS a wajen birnin Mosul.
Wani jirgin yakin Iraqi, yayin luguden bama-bamai akan mayakan kungiyar ISIS a wajen birnin Mosul. Reuters

Rundunar sojin Iraqi ta kaddamar da farmakin jiragen yaki kan mayakan kungiyar IS da ke cikin Syria.

Talla

Rundunar sojin Iraqi ta ce an kaddamar da sabon farmakin ne bisa umarnin da amincewar shugaban Syria Bashar al-Assad da kuma rundunar sojin da Amurka ke jagoranta wajen yakar kungiyar ta IS.

Iraqi dai na da kyakkyawar dangantaka da kasashen Iran da Rasha, wadanda suka kasance manyan kawayen shugaba Assad, zalika a lokaci guda, Iraqi na samun goyon bayan hadar rundunar sojin da Amurka ke jagoranta a kasar ta Syria.

A watan Disambar bara Fira Ministan Iraqi Haidar al-Abadi ya sanar da murkushe mayakn IS a fadin kasar, to sai dai mayakan sun ci gaba da kai hare-haren kunar bakin wake cikin kasar ta Iraqi, daga maboyarsu da ke kan iyakarta da Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.