Thailand: Jami'an agaji sun ceto dalibai 6 daga cikin 12 da ke makale a kogo

Jami'an agaji a arewacin Thailand yayin kokarin ceto daliban da suka shafe sama da makwanni 2 a makale a cikin kogo.
Jami'an agaji a arewacin Thailand yayin kokarin ceto daliban da suka shafe sama da makwanni 2 a makale a cikin kogo. ©FACEBOOK/ANYAWUT PHO-AMPAI/via REUTERS

Masu linkaya sun yi nasarar ceto shidda daga cikin dalibai shabiyu da malaminsu guda, da suka shafe fiye da makwanni 2 makale cikin wani kogo a arewacin kasar Thailand, sakamakon ambaliyar ruwan da ta mamaye hanyar shigarsa.

Talla

Shugaban tawagar masu aikin ceton Laftanat Janar Kongcheep tantrawanit, ya ce tuni daliban biyu suka isa sansanin da jami’an ceton suka kafa a gaf da inda tawagar daliban ta makale.

A ranar 23 ga watan Yuni da ya gabata, daliban 12 masu shekaru tsakanin 11 zuwa 16 tare da malamin horar da su kwallon kafa mai shekaru 25, suka makale cikin wani kogo da suka shiga somin fakewa ruwan sama da ya fara sauka, wanda daga bisani kuma ruwan ya mamaye tsukakkiyar hanyar shiga kogon.

Kwararrun masu linkaya daga kasashen duniya 13 ne aka gayyato inda suka aiki tare da wasu kwarrun masu linkayar ‘yan kasar Thailand domin ceto yaran da kuma malaminsu.

Shugaban tawagar masu aikin ceton Narongsak Osottanakorn ya ce tilas ne suka kara kaimi wajen gagawar zakulo yaran, la’akari da cewa nan gaba kadan akwai yiwuwar ci gaba da saukar ruwan sama, lamarin da babu shakka zai mayar da hannun agogo baya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.