Rasha-China

Rasha da China sun ki yarda da karin takunkumai kan Korea ta Arewa

Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin yayin zaman majalisar kan shirin lalata makaman nukiliyar Korea ta Area.
Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya Vitaly Churkin yayin zaman majalisar kan shirin lalata makaman nukiliyar Korea ta Area. © Reuters

Kasashen China da Rasha sun bukaci karin lokaci don nazartar bukatar da Amurka ta shigar gaban Majalisar Dinkin Duniya game da dakatar da duk wata jigilar man fetur zuwa Korea ta arewa.

Talla

Bukatar ta kasashen China da Rasha game da neman karin lokaci don nazartar batun na sanya takunkumin shigar da Man fetur Korea ta Arewa na zuwa ne kwana guda gabanin ganawar Mike Pompeo da kwamitin tsaro na Majalisar dinkin Duniya kan shirin Korea na lalata makamanta na Nukiliya.

A makon da ya gabata ne dai Amurkan ta shigar da bukatar gaban kwamitin sanya takunkumi na Majalisar inda ta bukaci daukar matakin haramta shigar da mai Korea ta Arewa sakamakon karya dokar da ta yi na shigar da man da ya wuce wanda aka kayyade mata shigarwa a kowacce shekara.

A bara ne dai Majalisar Dinkin Duniyar ta cimma matsaya kan adadin man da za a rika shigarwa koriya ta arewan inda ta gindaya cewa matukar kasar ta haura adadin ganga dubu dari biyar kowacce shekara ta saba ka’ida.

A cewar Amurka Koriyan ta zarta adadin man da aka kayyade mata ta shigar da shi kasar duk shekara a bara.

Kasashen na China da Rasha wadanda ke matsayin kawaye ga Kim Jong Un su ne ja gaba wajen shigar da man koriya ta arewa.

Amurkan dai na zargin cewa Korea ta arewan ta yi dakon mai da yawanshi ya kai ganga dubu dari bakwai da 59 da 793.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.