Korea ta kudu

Park Guen Hye na fuskantar zaman shekaru 32 a yari

Park Geun-hye tsohuwar Shugabar kasar Koriya ta kudu
Park Geun-hye tsohuwar Shugabar kasar Koriya ta kudu REUTERS/Kim Hong-Ji

Wata kotu a kasar Koriya ta Kudu ta sake yankewa tsohuwar shugabar kasar Park Guen Hye hukuncin daurin karin shekaru 8 saboda karbar wasu kudade daga jami’an tsaro ta hanyar da basu kamata ba.

Talla

Tsohuwar shugabar kasar taki halartar zaman kotu na yau, wanda alkali ya same ta da laifin karbar Dala miliyan kusan 3 daga cikin kudaden hukumar leken asirin kasa.

Kotun tace ta daure Hye shekaru 6 a gidan yari saboda karbar kudaden da kuma karin shekaru 2 saboda laifuffukan zabe.

Da wannan hukunci na yau, yanzu haka tsohuwar shugabar kasar mai shekaru 66 na fuskantar yin shekaru 32 a gidan yari.

Uwargida Park da aka tsige daga mulki na fuskantar tuhume-tuhume kan cin hanci da rashawa da tozarta karfin mulki da kuma fallasa sirrikan kasa.

Ana zargin Park Geun-hye da hada kai da aminiyarta, Choi Soon-sil wajen karbar kudade daga wasu manyan kamfanonin kasar da suka hada da Samsung da nufin yi mu su alfarmar siyasa.

Koriya ta Kudu na da damar yanke hukuncin rai-da-rai ga duk wanda aka samu da laifin cin hanci da rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.