Jordan za ta rarraba ma'aikatan agajin Syria 800 zuwa kasashen turai 3

Wasu motocin safa dauke da mayakan 'yan tawaye tare da iyalansu, da suka fice daga yankin Deraa, da ke Kudu maso yammacin Syria.
Wasu motocin safa dauke da mayakan 'yan tawaye tare da iyalansu, da suka fice daga yankin Deraa, da ke Kudu maso yammacin Syria. REUTERS/Khalil Ashawi

Gwamnatin Jordan a dazun nan ta ce ta karbi ma’aikatan agaji na kungiyar White Helmets 800 tare da iyalansu daga hannun Isra’ila.

Talla

A yau Lahadi 22 ga watan Yuli na 2018, Isra’ila ta sanar da kwashe ma’aikatan agajin na White Helmets da suka tsere daga yankunan ‘yan tawaye, biyo bayan farmakin sojin Syria a yankunan.

A halin yanzu kasar ta Jordan ta ce tuni ta fara shirin rarraba jami’an agajin zuwa wasu kasashen yammacin turai, da suka hada da Birtaniya, Canada da kuma Jamus, tuni kuma ta bukaci taimakon majalisar dinkin duniya wajen aiwatar da shirin.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Jordan Muhammad al-Kayed ya ce ma’aikatan agajin zasu ci gaba da zama kasar, har zuwa lokacin da za a kammala shirin rarraba su zuwa kasashen na Birtaniya, Canada da kuma Jamus, cikin watanni uku masu zuwa.

A shekarar 2013 aka kungiyar agajin ta White Helmets, da ke gudanar da ayyukan bada agajin gaggawa ga wadanda suka jikkata sakamakon farmakin jiragen yaki, da na sojin kasan Syria da kawayenta a yankunan da ‘yan tawaye ke iko da su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.