Afghanistan-Taliban

Hare-haren IS da Taliban na barazana ga zaben Afghanistan - MDD

Wasu tarin masu aikin kai ceto a birnin Kabul na Afghanistan bayan harin ranar Lahadi 22 ga watan Yuli da Taliban ta kai gab da filin jirgin saman birnin.
Wasu tarin masu aikin kai ceto a birnin Kabul na Afghanistan bayan harin ranar Lahadi 22 ga watan Yuli da Taliban ta kai gab da filin jirgin saman birnin. REUTERS/Omar Sobhani

Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya yayi Allah wadai da tahsin hankalin da kungiyar Taliban da kuma IS ke amfani da shi wajen hana shirin zaben kasar da za’ayi nan gaba.

Talla

Matakin na zuwa ne kwana guda bayan kazamin harin kunar bakin waken da ya hallaka mutane 23, ya kuma jikkata wasu da dama a birnin Kabul.

Ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Afghanistan ya ce akalla mutane 1,700 hare-haren ta'addancin ya kashe cikin watanni 6 da suka gabata, kuma sama da rabin su sun mutu ne sakamakon harin kungiyar IS yayin da  wasu kuma suka mutu sakamakonn na Taliban.

Akalla mutane miliyan 9 suka yi rajistar zaben da za’ayi ranar 20 ga watan Oktoba, cikin su har da mata miliyan 3.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.