Syria

ISIS ta kashe mutane sama da 200 a Syria

Ba a karon farko kenan ba da ake kaddamar da kazamin hari a lardin Sweida na Syria
Ba a karon farko kenan ba da ake kaddamar da kazamin hari a lardin Sweida na Syria Sana/Handout via REUTERS

Wasu jerin hare-hare da suka hada da na kunar bakin wake da kungiyar ISIS ta kaddamar, sun yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 220 a kudancin Syria, abin da aka bayyana a matsayin daya daga cikin hare-hare mafi muni a kasar.

Talla

Kungiyar da ke sanya ido kan hakkin bil’adama a Syria ta ce, hare-haren sun shafi yankuna da dama da ke karkashin ikon gwamnati a lardin Sweida.

Kungiyar ISIS ta dauki alhakin munanen hare-haren, in da ta ce, dakarunta sun far wa wuraren da ke karkashin ikon gwamnati da suka hada da kananan sansanonin jami’an tsaro a birnin Sweida.

Kungiyar da ke sanya ido a kasar ta ce, ‘yan kunar bakin wake hudu ne suka tayar da bama-baman da suka yi damara da su a Sweida, yayin da sauran maharan suka far wa kananan kauyuka tare da harbe jama’ar da ke zaune a cikin gidajensu.

Ba a karon farko kenan ba da ake kai farmaki kan birnin Sweida tun bayan da kasar ta Syria ta fada cikin yaki a shekarar 2011.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.