Laos-Cambodia

'Yan Cambodia na gujewa gidajensu bayan ballewar Dam a Laos

Yanzu haka dai hukumomin kasar ta Cambodia na ci gaba da aikin kwashe mutanen da garuruwansu ke gab da kan iyakar kasar da Laos ta ruwa don tseratar da rayukansu.
Yanzu haka dai hukumomin kasar ta Cambodia na ci gaba da aikin kwashe mutanen da garuruwansu ke gab da kan iyakar kasar da Laos ta ruwa don tseratar da rayukansu. ABC Laos News/Handout via REUTERS

Dubban jama’a a kasar Cambodia su tsere daga gidajensu, biyo bayan ballewar katafaren Dam na kasar Laos, wanda ruwansa ya kwarara zuwa yankunan da ke kan iyakar kasashen biyu.

Talla

Ballewar katafaren Dam din na Laos, ne ya sabbaba sauya hanyar da ruwa ke kwarara zuwa yankin kudancin kasar da ruwan ya shafe tsawon lokaci baya bi tun bayan gina madatsar ruwan, hakan ya tilastawa mazauna kauyukan kasar Cambodia da ke kan iyaka da kasar ta Laos ta sashin kudanci tserewa muhallansu.

Wani mai magana da yawun gwamnatin kasar ta Cambodia, ya ce sojin kasar sun dukufa wajen kwashe jama’ar kauyukan da ke kan hanyar ruwan bisa kananan jiragen ruwa, da kuma ayyukan raba kayyakin agaji.

A kasar Laos kuwa zuwa yanzu jami’an agaji sun tabbatar da mutuwar mutane 27, yayinda jami’an ceto ke ci gaba da neman wasu 131 da suka bace a ambaliyar ruwan da ta biyo bayan fashewar madatsar ruwan da aka gina kan dala biliyan daya da miliyan 200, bisa hadin gwiwar wasu kamfanonin Korea, Thailand da kuma kasar ta Laos.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.