Indonesia

Mutane dubu 20 sun rasa matsugunarsu a Indonesia

Adadin wadan da suka hallaka sakamakon girgizar kasa mai karfin gaske da ta auku a yankin tsibirin Lombok na kasar Indonesia, ya haura dari, yayin da jami’an agaji suka sake shafe  daren suna aikin lalibo masu sauran numfashi cikin gidaje, makarantu da kuma wuraren ibada.

masu aikin ceto a kasar Indonesia na kokarin zakulo masu sauran numfashi a karkashin ginin Masallacin da ya rushe
masu aikin ceto a kasar Indonesia na kokarin zakulo masu sauran numfashi a karkashin ginin Masallacin da ya rushe Reuters/路透社
Talla

Mahukuntar Indonesia sun tabbatar da mutuwar mutane fiye da dari, yayin da wasu sama da maitan suka jikkata, kazalika, an kiyasta cewar mutane fiye da dubu 20,000 ne suka rasa muhallansu, sakamakon girgizar kasar mai karfin maki kusan 7.

Da akwai fargabar karuwar adadin wadanda suka hallaka,duba da yadda jami’an agaji ke amfani da injunan daga baraguzai a wani masallaci da ya rushe kuma ake ganin da mutane a ciki.

Silverius Tasman, wani  jami’in agaji  a wata kungiya mai zaman kanta mai alaka da kungiyar Save the Children, wanda ya ziyarci kauyen Karan Bajo dake Arewacin tsibirin, ya ce, yawancin mutanen da suka rasa muhallansu na zaune a matsugunnan wucin gadi ko a gefen hanya.

Acewar Tasman, mutanen na cikin muwuyancin hali, na bukatun ruwan sha da na abinci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI