Girgizar kasa ta sake afkawa tsibirin Lombok
Wallafawa ranar:
Girgizar kasa mai karfin maki 5.9 ta sake afkawa tsibirin Lombok na kasar Indonesia a yau Alhamis, karo na uku cikin kasa da makwanni biyu.
Lamarin dai ya jefa dubban jama’ar da ke gudun hijira a sansanonin wucin gadi cikin tashin hankali, la’akari da cewa kwanaki hudu da suka gabata wata girgizar kasa mai karfin maki 7 a ma’auninta na Ritcher ta hallaka sama da mutane 160.
Cibiyar bincike al’amuran karkashin kasa ta Amurka ta ce, girgizar kasar ta auku ne a arewa maso yammacin tsibirin na Lombok, a dai dai lokacin da jami’an agaji ke kokarin ceto ragowar wadanda suka rayu daga cikin baraguzan ginin da suka rushe, bayan girgizar kasa mai karfin maki 7 da ta afkawa tsibirin a ranar Lahadi, 5 ga watan Agusta na 2018.
Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa ya rawaito cewa, girgizar kasar ta yau Alhamis ta jefa matukar tsoro a zukatan mazauna tsibirin, inda a lardin Tanjung mutane suka rika ficewa daga ababen hawansu akan tituna suna guje guje cikin dimuwa.
Kakakin hukumar bada agajin gaggawa ta Indonesia Sutopo Purwo Nugroho ya shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa cewa, mutane 164 suka rasa rayukansu a girgizar kasar da ta auku a ranar Lahadin da ta gabata.
Nugroho ya kara da cewa mutane 1, 400 suka jikkata yayinda girgizar kasar ta raba sama da mutane dubu 150, 000 da muhallansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu