Syria

Putin ya bukaci kudaden sake gina Syria daga kasashen Turai

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin.
Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin. REUTERS/Sergei Karpukhin

Shugaban Rasha Vladmir Putin ya bukaci kasashen turai da su bayarda gudunmawar kudaden da za’a yi amfani da su wajen sake gina kasar Syria da yaki ya dai-daita, domin baiwa miliyoyin ‘yan kasar da ke gudun hijira damar komawa gida.

Talla

Putin wanda yayi wannan kira gabannin ganawarsa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a yau Lahadi, ya ce gudunmawar za ta taimaka wajen rage matsalar yawaitar kwarar ‘yan gudun hijirar da kasashen turai ke kokarin maganacewa.

Shugaban na Rasha ya ce a halin da ake ciki, akwai ‘yan kasar Syria akalla miliyan daya da ke gudun hijira a Jordan, sai kuma wasu ‘yan kasar ta Syria miliyan guda da ke Lebanon.

A kasar Turkiya kadai kuwa shugaba Putin ya ce yawan ‘yan Syria da ke gudun hijira a kasar ya kai miliyan uku.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.