Dubban 'yan gudun hijirar kabilar Rohingya sun yi zanga-zanga

Dubban 'yan gudun hijirar kabilar Rohingya, yayin gudanar da zanga-zanga a sansaninsu da ke kasar Bangladesh.
Dubban 'yan gudun hijirar kabilar Rohingya, yayin gudanar da zanga-zanga a sansaninsu da ke kasar Bangladesh. REUTERS/Mohammad Ponir Hossain

Dubban ‘yan gudun hijirar kabilar Rohingya sun gudanar da zanga-zanga a yau Asabar, inda suke neman a bi musu hakkinsu kan cin zarafin da sojojin Myanmar suka yi musu da sunan farmakin murkushe ‘yan ta’adda a jihar Rakhine.

Talla

‘Yan kabilar ta Rohingya Musulmi sun gudanar da zanga-zangar ce a dai dai lokacin da yau Asabar aka cika shekara guda, da tsrewar da suka yi daga Myanmar zuwa Bangladesh son gujewa farmakin da sojin Myanmar suka kaddamar kansu.

Yawan ‘yan gudun hijirar da suka yi zanga-zangar ta yau ya kai kimanin akalla dubu 40.

Zuwa karshen shekarar bara, kididdiga ta nuna cewa yawan Muslmin ‘yan kabilar ta Rohingya da suka tsere zuwa Bangladesh daga Myanmar ya haura dubu 700.

Farmakin da sojin na Myanmar suka kaddamar kan kabilar ta Rohingya a ranar 25 ga watan agustan 2017, ya biyo bayan hare-haren da wasu mayaka masu rajin ‘yantar da ‘yan kabilar suka kai kan jami’an tsaron kasar.

Kungiyar likitocin kasa da kasa ta Medecins Sans Frontiers ta ce a ranar farko da sojin na Myanmar suka kaddamar da farmakin kadai, sun hallaka fararen hular kabilar ta Rohingya Muslmi kusan dubu 7.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.