Myanmar

Kasashen Duniya sun bukaci kama shugabannin sojojin Myanmar

Babban kwamandan sojan Myanmar Janar Min Aung Hlaing
Babban kwamandan sojan Myanmar Janar Min Aung Hlaing REUTERS/Ann Wang/File Photo

Amurka ta jagoranci jerin kasashen Duniya da dama da suka bukaci kama shugabannin sojojin Myanmar da laifi na kisan kiyashin da suka yiwa yan kabilar Rohingya Musulmi wajen gurfanar da su a kotun Duniya.

Talla

Jakadiyar Amurka a kwamitin sulhu Nikki Haley tace ya zama dole ayi magana kan kisan kiyashin da aka yiwa yan kabilar Rohingya Musulmi sama da 10,000 domin duniya taji.

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres yayi tsokaci kan sakamakon binciken da aka gudanar,Guterres ya bayyana cewa ya na da yakinin cewar sakamakon wannan bincike da kuma shawarwarin da aka bayar na bukatar nazari sosai daga dukkan hukumomin Majalisar Dinkin Duniya. Hadin kan kasashen duniya nada matukar muhimmanci domin ganin an tabbatar da sahihanci a bayyane, ba kuma tare da nuna son kai ba wajen samun bayanan gaskiya .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.