China- Majalisar Dinkin Duniya

Majalisar Dinkin Duniya ta damu da tsare musulmi milyan 1 a China

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan yadda hukumomin China ke tsare da 'yan kabilar Uighur Musulmi kusan miliyan guda a karkashin wani shiri na yaki da ta’addanci.

Majalisar ta bukaci gaggauta sakin mutanen su kusan Milyan 1 ko da dai hukumomin na China sun ce suna ci gaba da tsare su ne saboda barazanar da su ke da shi ga tsaron kasar.
Majalisar ta bukaci gaggauta sakin mutanen su kusan Milyan 1 ko da dai hukumomin na China sun ce suna ci gaba da tsare su ne saboda barazanar da su ke da shi ga tsaron kasar. Yuri KADOBNOV / AFP
Talla

Majalisar ta bukaci gaggauta sakin daukacin mutanen da ake tsare da su, yayin da 'yan Majalisun Amurka suka bukaci sanyawa manyan jami’an China takunkumi kan tsare mutanen a Yankin Xinjiang.

Kasar China taki amincewa da zargin, inda ta ke cewa wadanda ta kama masu tayar da hankali ne a Yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI