India

Kotun kolin India ta halatta auren jinsi

Kotun kolin Indiya ta halata auren jinsi, a kasar da ta kasance ta 2 mafi yawan al’umma a duniya, matakin na tarihi da ya kawo karshen haramcin da kasar ke amfani da shi tun cikin karni na 15.Babbar kotun kasar da ke kudancin asiya mai yawan al’umma biliyan 1,25  ta soke dokar haramta auren jinsi wadda shugaban kotun kolin kasar Dipak Misra ya ce tana matsayin wani makamin nuna kyamar masu auren jinsi a kasar.

Bayan gwagwarmayar tsawon kusan shekaru 20 da dokar shara ta 377 da ta haramta duk wata alaka da ta danganci aure tsakanin mutane yan jinsi guda.
Bayan gwagwarmayar tsawon kusan shekaru 20 da dokar shara ta 377 da ta haramta duk wata alaka da ta danganci aure tsakanin mutane yan jinsi guda. REUTERS/Francis Mascarenhas
Talla

Hotunan da tashoshin talabijin din kasar ta Indiya suka yada, sun nuna yan gwagwarmayar nema kare hakkin masu auren jinsin na kuka da hawayen farin ciki, a lokacin da ake karanta soke haramcin a kotun

A cikin kundin shara’ar da kasar ta Indiya ta gada daga turawan mulkin malakar kasar Birtaniya ana zartarwa masu auren jinsi hukumcin daurin zaman gidan yari na rai da rai ne. An kuma alakanta laifin auren na jinsi da na nuna kabilanci

Bayan gwagwarmayar tsawon kusan shekaru 20 da dokar shara ta 377 da ta haramta duk wata alaka da ta danganci aure tsakanin mutane yan jinsi guda.

A cikin watan Yulin da ya gabata ne wasu alkalai na kotun kolin su 5 suka saurari hujojin da masu auren jinsin suka gabatar masu, mutanen da suka hada da wasu fitattun mutane a kasar ta Indiya, da suka nuna goyon bayan soke dokar da suka ce ta sabawa kundin tsarin mulkin kasar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI