Myanmar-ICC

Myanmar ta yi watsi da hukuncin ICC kan 'yan Rohingya

Shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi.
Shugabar gwamnatin Myanmar Aung San Suu Kyi. Mark Metcalfe/Pool via REUTERS

Myanmar ta yi watsi da hukuncin kotun hukunta manyan laifuka ICC ta zartas na fara bincike kan cin zarafi da kisan kiyashin da kasar ta yiwa musulmi ‘yan kabilar Rohingya ba tare da kasancewar kasar mamba a cikin kwamitin ba.

Talla

A wani hukuncin bazata da kotun ta yanke jiya Alhamis ta bayar da umarnin fara binciken zargin yunkurin shafe kabilar ta Rohingya da ake yi kan gwamnatin kasar ta hannun dakarun sojinta.

Sai dai a martinin Mynamar yau Juma’a ta ce babu ta yadda za ayi kasar ta mutunta hukuncin kotun wanda bai tasamma adalci ba.

Cikin sanarwar da ta fitar, Myanmar ta yi zargin cewa ICC ta yanke hukuncin ne ba tare da cikakken bincike a fayyace ba, face bisa bayanan da ta samu daga bangare daya.

Hukuncin kotun dai na nufin cewa, babban mai shigar da kara na ICC zai jagoranci gudanar da bincike a kasar ta Myanmar ko da ba tare da sahalewarta ba.

Baya ga cin zarafi da kuma kisan kiyashin da Myanmar ta yi wa ‘yan Kabilar ta Rohingya da ke jihar Rakhine wanda ya tilasta fiye da musulman miliyan guda tserewa makociyar kasar Myanmar, ta kuma hana ‘yan jarida da jami’an tsaro ziyartar jihar don ganewa idonsu abin da ke faruwa, yayinda ta ke ci gaba da tsare wasu ‘yan jarida biyu da suka wallafa labara kan halin da tsirarun musulman ke ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.