Sojin Yemen sun hallaka 'yan tawayen Houthi 73 cikin kwanaki 2
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce wani harin dakarun sojin Yemen a gabashin birnin Hodeida ya hallaka ‘yan tawayen Houthi 73 tsakanin jiya asabar da yau Lahadi, bayan gaza cimma matsaya a taron sasanta rikicin kasar da ya gudana a Geneva ranar Juma’a.
Tashar talabijin ta Al-Ekhbariya mallakin Saudiyya ta ce yayin sumamen karkashin jagorancin rundunar Amaliqa dakarun na Yemen sun kame tarin ‘yan tawayen ciki har da wasu jagororinsu baya ga kwace tarin makamai, ko dai an hallaka wasu soji 11 baya ga jikkata wasu 17.
Haka zalika majiyar ta ce sojin sun kuma taimaka wajen tseratar da tarin fararen hula da ke yanki yankin wanda ‘yan tawayen suka yiwa kawanya.
A juma'ar da ta gabata ne bangarorin biyu suka gaza cimma matsaya a tattaunawar da Majalisar Dinkin Duniya ke shiga tsakani da ta gudana a birnin Geneva, ko da dai Yemen ta dora alhakin lalacewar tattaunawar kan 'Yan tawaye wadanda ta ce sun gaza halarta kamar yadda aka tsara.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu