China-HRW

China na azabtar da musulmi 'yan kabilar Uighur -HRW

Kusan za a iya cewa China ta yi kaurin suna wajen take hakkin bil'adama musamman a al'amuran da suka shafi wadanda suka karya dokokinta.
Kusan za a iya cewa China ta yi kaurin suna wajen take hakkin bil'adama musamman a al'amuran da suka shafi wadanda suka karya dokokinta. 路透社

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Right Watch ta bukaci sanyawa China takunkumai kan yadda ta ke ci gaba da tsare da tsirarun musulmai ‘yan kabilar Uighur kusan miliyan guda a gidajen yari.Kiran na Human Right Watch na zuwa ne wata guda bayan Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci gaggauta sakin tsirarun musulman.

Talla

Kungiyar ta Human Right Watch ta ce kamata ya yi kasashen duniya su sanya takunkumai kan China game da yadda ta yi biris da kiraye-kirayen da ake mata na sakin mutanen su kusan miliyan guda wadanda ta ke zargi da tayar da rikici.

A watan da ya gabata Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa kan yadda hukumomin China ke ci gaba da tsare 'yan kabilar ta Uighur Musulmi a karkashin wani shirin kasar na yaki da ta’addanci.

Akwai dai kiraye-kiraye daga kungiyoyin kare hakkin bil’adama da kuma Majalisar na ganin lallai China ta gaggauta sakin daukacin mutanen, kazalika wasu mambobin Majalisun Amurka sun bukaci sanyawa manyan jami’an China takunkumi kan tsare mutanen a Yankin Xinjiang.

Ko dai China ta ki amincewa da zargin, inda ta ke cewa wadanda ta kama masu tayar da hankali ne a Yankin, kuma tana daukar matakan ganin ta dakile duk wani yunkurin ta’addanci a kasarta.

Akwai dai rahotanni da ke cewa tsirarun musulmin su kusan milyan guda na fuskantar mabanbantan azabtarwa daga hukumomi a gidajen yarin da suke tsare da ke yankin na Xinjiang.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI