Syria-Faransa

Faransa na fargabar bazuwar yan ta'adan Syria a duniya

Ministan harakokin wajen Faransa  Jean-Yves Le Drian, a 1 ogusta  2018.
Ministan harakokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian, a 1 ogusta 2018. (JEAN-CHRISTOPHE BOURDILLAT / RADIO FRANCE)

Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya ce harin da dakarun Syria suka kaddamar kan lardin Idlib, zai yi sanadiyyar watsuwar ‘yan ta’adda a kasashen ketare, kuma hakan ba karamar barazana ba ce ga tsaron kasashen Yammacin duniya.

Talla

Le Drian wanda ke zantawa da tashar talabijin ta BFMTV, ya ce tabbas akwai dimbin Faransawa da ke Syria a matsayin masu jihadi tare da sauran kungiyoyin ta’addanci a yankin na Idlib.

Hakazalika ministan ya ce akwai wasu mayakan ‘yan asalin kasashe daban daban da ke yaki a Syria, abin da ke nufin cewa, kaddamar da farmaki akan su zai yi sanadiyyar su kwarara tare sa haddasa barazanar tsaro ga sauran kasashen duniya.

Ministan harkokin wajen na Faransa ya ce, har yanzu akwai mafita domin hana faruwar hakan, kuma daya daga cikin hanyoyin da za a bi a cewarsa ita ce mara wa yunkurin da Turkiyya ke yi domin dakatar da farmakin na Rasha da Syria a kan yankin na Idlib.

Daga shekara ta 2015 zuwa yau, Faransa ce kasar da ta fi fuskantar hare-haren ‘yan ta’adda a yankin Turai baki dayansa, wannan ne ma ya sa minista Le Drian ke cewa, adadin ‘yan ta’adda da suka tsere daga Idlib kafin ko kuma a lokacin wannan farmaki ya kama daga dubu 10 zuwa dubu 15.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI